Skip to content
التوبَة /

Aya 28

9 : 28

Aya 28 of التوبَة (9 : 28). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

التوبَة Ayoyi 129
9 : 28

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡمُشۡرِكُونَ نَجَسٞ فَلَا يَقۡرَبُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ بَعۡدَ عَامِهِمۡ هَٰذَاۚ وَإِنۡ خِفۡتُمۡ عَيۡلَةٗ فَسَوۡفَ يُغۡنِيكُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦٓ إِن شَآءَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai Alfarma a bãyan shẽkarar su wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalar Sa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima.

Explanation & meanings · 1
  1. Idan kun ji tsõron talauci sabõda hanã mushirikai zuwa hajji sabõda fataucinku da su zai rage, to, bãbu kõme, arziki ga Allah yake, Yanã bãyar da shi ga wanda Yake so.