Skip to content
الأعرَاف /

Aya 145

7 : 145
الأعرَاف Ayoyi 206
7 : 145

وَكَتَبۡنَا لَهُۥ فِي ٱلۡأَلۡوَاحِ مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡعِظَةٗ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ فَخُذۡهَا بِقُوَّةٖ وَأۡمُرۡ قَوۡمَكَ يَأۡخُذُواْ بِأَحۡسَنِهَاۚ سَأُوْرِيكُمۡ دَارَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai."

Explanation & meanings · 1
  1. Mafi kyau daga Attaura shi ne wanda yake bayyananne; watau kada a yi aiki da abin da yake bai bayyana ba, sai da abin da ya bayyana, bayan an yarda cewa dukansu daga Allah suke.