Skip to content
Jerin Surori /

المُجَادلة

المُجَادلة is chapter 58 of the Quran and has 22 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

22 Ayoyi Lambar Sura 58
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

قَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّتِي تُجَٰدِلُكَ فِي زَوۡجِهَا وَتَشۡتَكِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَٱللَّهُ يَسۡمَعُ تَحَاوُرَكُمَآۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٌ

Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.

Explanation & meanings · 1
  1. Wannan ƙissa tanã nũna cewa a Majalisar Annabi kõwa na da 'yancin shiga, namiji da mace, kuma ya faɗi abin da yake so, kõ da ya sãɓãwa abin da Annabi ya gani ƙãfin wani wahayi ya sauka. Gã wannan mace sunanta Khaulatu bnt Sa'alabah ta kai ƙãrar mijinta Ausu bn Samit wanda ya yi zihãri game da ita, watau ya ce idan ya kusance ta kamar ya kwãna da uwarsa ne. Ga al'adar lãrabãwa wannan bã saki bã ne, kuma ba ya iya kwana da ita har abada. Wannan shi ne takai ƙarã wurin Annabi har ta yi mahãwar da shi a kansa. Kuma wannan ƙissa tanã nũna gaskiyar Annabi, bai yi jawãbi ba ga abin da bai sãmi wahayi ba a kansa.

ٱلَّذِينَ يُظَٰهِرُونَ مِنكُم مِّن نِّسَآئِهِم مَّا هُنَّ أُمَّهَٰتِهِمۡۖ إِنۡ أُمَّهَٰتُهُمۡ إِلَّا ٱلَّٰٓـِٔي وَلَدۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَيَقُولُونَ مُنكَرٗا مِّنَ ٱلۡقَوۡلِ وَزُورٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.

وَٱلَّذِينَ يُظَٰهِرُونَ مِن نِّسَآئِهِمۡ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا قَالُواْ فَتَحۡرِيرُ رَقَبَةٖ مِّن قَبۡلِ أَن يَتَمَآسَّاۚ ذَٰلِكُمۡ تُوعَظُونَ بِهِۦۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa'an nan su kõma wa abin da suka faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna. Wannan anã yi muku wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.

فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ شَهۡرَيۡنِ مُتَتَابِعَيۡنِ مِن قَبۡلِ أَن يَتَمَآسَّاۖ فَمَن لَّمۡ يَسۡتَطِعۡ فَإِطۡعَامُ سِتِّينَ مِسۡكِينٗاۚ ذَٰلِكَ لِتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۗ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ

To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi.

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ كُبِتُواْ كَمَا كُبِتَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ وَقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Lalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa.