Skip to content
النِّسَاء /

Aya 94

4 : 94

Aya 94 of النِّسَاء (4 : 94). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 94

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا ضَرَبۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَتَبَيَّنُواْ وَلَا تَقُولُواْ لِمَنۡ أَلۡقَىٰٓ إِلَيۡكُمُ ٱلسَّلَٰمَ لَسۡتَ مُؤۡمِنٗا تَبۡتَغُونَ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ مَغَانِمُ كَثِيرَةٞۚ كَذَٰلِكَ كُنتُم مِّن قَبۡلُ فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡكُمۡ فَتَبَيَّنُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bã Musulmi kake ba." Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni. Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani.

Explanation & meanings · 1
  1. Bayãnin cewa ana ɗaukar wanda aka ji ya yi kalmar shahãda mumini, sai fa idan an ga ya yi wani aiki, ko aka ji ya yi wata magana wadda take warware ma'anar kalmar shahadar, bãbu kuma wani tãwĩli ko jãhilcin da yake iya zama uzuri ga mai shi.