30 : 55
وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُقۡسِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ مَا لَبِثُواْ غَيۡرَ سَاعَةٖۚ كَذَٰلِكَ كَانُواْ يُؤۡفَكُونَ
Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.
Explanation & meanings · 1
- Sa'a ta farko Rãnar Ƙiyãma,ta biyu ɗan lõkaci, watau ɗan lõkacin da suka sãmi hutun azãbar kabari a tsakãnin bũsar farko da ta biyu. Akwai munãsabar ƙaryarsu ta dũniya da ta Lãhira. Akwai munasabar dangantakar lafazin kalmomi.