29 : 61
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã?" Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su?
Explanation & meanings · 1
- Yãya ake karkatar da su daga hijira dõmin tsõron yankewar abinci, alhãli kuwa sun tafi wurin yardar wanda Ya halicci sammai da ƙasã? Yin hijira yanã a cikin jarrabãwar Allah ga Musulmi.