28 : 16
قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي فَٱغۡفِرۡ لِي فَغَفَرَ لَهُۥٓۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai.