Skip to content
البَقَرَة /

Aya 250

2 : 250

Aya 250 of البَقَرَة (2 : 250). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 250

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma a lõkacin da suka bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."

Explanation & meanings · 1
  1. Dãwũdu ɗan Ãisha ya gãji annabcin Shamwĩlu da mulkin Ɗãlũta, shĩ ne ya fãra haɗã su a cikin Bani lsrã'ila bãyansa sai ɗansa Sulaimãn ya gãje shi haka nan. Yawan mutãnen Ɗãlũta da suka yi yãƙi kamar adadin mutãnen Badar ne waɗanda suka yi yãƙi tãre da Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.