Skip to content
البَقَرَة /

Aya 193

2 : 193
البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 193

وَقَٰتِلُوهُمۡ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتۡنَةٞ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ لِلَّهِۖ فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَلَا عُدۡوَٰنَ إِلَّا عَلَى ٱلظَّٰلِمِينَ

Kuma ku yãƙe su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.

Explanation & meanings · 1
  1. An umurci Musulmi da tsõkana ga kãfiran da suke nũna musu ƙiyayya bayyane, dõmin su hana su yin addininsu da kyau, kamar yadda Allah Ya umurce su, suna fitinar su da wahalõli. Kuma kada ku bar su, su laɓe da wani watan alfarma kõ hurumi, duk yadda hãli ya yi, a yi haka nan, alfarmõmi nã da ƙisãsi.