14 : 28
۞ أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ بَدَّلُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ كُفۡرٗا وَأَحَلُّواْ قَوۡمَهُمۡ دَارَ ٱلۡبَوَارِ
Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?
Explanation & meanings · 1
- Kuraishãwa wadanda Allah Ya yi musu ni'imar zama a cikin hurumin Allah da aminci da Ya zuba a kansu da albarku, sun musanya gõdiya da kãfirci a lõkacin da suka ƙaryata Manzon Allah. Sun saukar da mutãnensu a gidan halaka a Badar.