Skip to content
الرَّعد /

Aya 14

13 : 14
الرَّعد Ayoyi 43
13 : 14

لَهُۥ دَعۡوَةُ ٱلۡحَقِّۚ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَجِيبُونَ لَهُم بِشَيۡءٍ إِلَّا كَبَٰسِطِ كَفَّيۡهِ إِلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَٰلِغِهِۦۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ

Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama ba fãce yanã a cikin ɓata.

Explanation & meanings · 1
  1. Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗanda kõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã neman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa.