Skip to content

أبو طالب عبد مناف بن عبد المطلب

الإسم

Abu Ɗalib Abdu Manaf ɗan Abdulmuɗɗalib

اسم الشهرة

Abu Ɗalib

نبذة مختصرة

Abdu Manaf (Imrana) ɗan Abdulmuɗɗalibi ɗan Hashim, alkunyarsa ita ce Abu Ɗalib, kuma wannan alkunya ta rinjaye shi, har ma ba a san wani yana kiran sa da Abdu Manaf ba. Shi ne baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mafi kusanci, kuma shaƙiƙin mahaifinsa (uwa ɗaya uba ɗaya), wanda ya ɗauki nauyinsa, ya raine shi, kuma ya taimake shi, sannan shi ne mahaifin Aliyu - Allah Ya yarda da shi - da sauran 'yan'uwansa. Ya kasance ɗaya daga cikin jaruman Banu Hashim kuma shugabanninsu, sannan yana daga cikin fasihan masu huɗuba, masu hankali kuma masu ƙin ƙasƙanci. Sai dai ya mutu a matsayin kafiri, kuma babu wani saɓani abin lura a kan hakan a tsakanin ma'abota ilimi. Haƙiƙa Imam Muslim ya ruwaito daga Abu Hurairah ya ce: A lokacin da mutuwa ta zo wa Abu Ɗalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zo masa, sai ya ce: (Ya baffana, ka ce 'La ilaha illallah', kalmar da zan yi maka shaida da ita a Ranar Ƙiyama). Sai ya ce: Ba don gudun kada Ƙuraishawa su zage ni su ce: Babu abin da ya sanya shi faɗarta sai tsoron mutuwa ba, da na faranta maka rai da ita, kuma ba don komai zan faɗe ta ba sai don na faranta maka rai da ita. Sai Allah - Mai girma da buwaya - Ya saukar da cewa: (Lallai kai ba ka shiryar da wanda ka so, amma Allah ne Yake shiryar da wanda Ya so, kuma Shi ne Mafi sani ga masu shiryuwa). Imamul Bukhari da Muslim sun ruwaito daga hadisin Abbas ɗan Abdulmuɗɗalibi cewa ya ce: Na ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mene ne ka amfanar da baffanka, domin kuwa ya kasance yana ba ka kariya kuma yana yin fushi saboda kai? Ya ce: (Yana cikin wuta mara zurfi, kuma ba don ni ba, da ya kasance a mataki mafi ƙasƙanci na wuta). Kuma Imam Muslim ya ruwaito daga hadisin Ibn Abbas cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Mafi sauƙin azaba a cikin 'yan wuta shi ne Abu Ɗalib, yana sanye da takalma biyu waɗanda kwakwalwarsa ke tafasa saboda su). Kuma an ruwaito daga Abu Sa'id cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an ambaci baffansa a wajensa, sai ya ce: (Wataƙila ceto na zai amfane shi a Ranar Ƙiyama, a sanya shi a cikin wuta mara zurfi wadda za ta kai idon sawunsa, wadda kwakwalwarsa za ta riƙa tafasa daga gare ta). Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. Ya rasu a shekara ta goma bayan aiko Annabi, kuma a tare da shi ne Khadija - Allah Ya yarda da ita - ta rasu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi baƙin ciki, wanda aka sanya wa shekarar sunan Shekarar Baƙin Ciki.

المراجع

Kari (1)
Sahih Al-Bukhari (5/ 52، ح3883، 3885، صحيح مسلم (1/ 195 ح209، 210، 212)، (1/ 55 ح25)، السيرة الحلبية (1/ 488)، الأعلام للزركلي (4/166).