عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (23)
"Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har ya kai {Suke aikatawa}".
Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".
Ingantacce ne a baki dayan hanyoyin sa Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
«Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan shine muslmin da yake da alƙawarin Allah da alƙawarin ManzonSa, dan haka kada ku warware alƙawarin Allah».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne".
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya cewa Baffansa; "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama", ya ce: Da badan Kuraishawa zasu aibatani ba, zasu ce: Razani da tsoron mutuwa ne suka kai shi haka ba da na faranta ranka da ita. Sai Allah Ya saukar: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda ka so ba saidai Allah Yana shiryar da wanda yake so} [Al-Kasas; 56].
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi