Skip to content

Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni

Daga Ma'ƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

"Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni".

«الْعِبَادَةُ فِي الْهَرْجِ كَهِجْرَةٍ إِلَيَّ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunar zuwa ibada da yin riƙo da ita a cikin zamanin rashin zaman lafiya da fitina da yaƙe-yaƙe da cakuɗewar al'amuran mutane, kuma cewa ladanta kamar hijira ce zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, hakan domin cewa mutane suna rafkana daga gareta, suna shagaltuwa daga gareta, babu mai ƙoƙari gareta sai ɗaiɗaiku.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Kwaɗaitarwa akan ibada da fuskanta zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - a kwanukan fitintinu; dan neman kariya daga fitintinu, da kuma kiyayewa daga ɓarna.

Bayanin falalar ibada a lokutan fitintinu da lokutan rafkana.

Yana kamata ga musulmi ya kaucewa guraren fitintinu da rafkana.

Manazarta

Sahih Muslim (4/ 2268) (2948).

Kari (4)

كشف المشكل من حديث الصحيحين (2/ 42).

البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (45/ 5).

بهجة الناظرين (2/ 455).

نزهة المتقين (ص942).