Skip to content

Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna

Daga Abu Katada AsSulami - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

"Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".

«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ فَلْيَرْكَعْ رَكْعَتَيْنِ قَبْلَ أَنْ يَجْلِسَ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kwaɗaitar da wanda ya zo masallaci ya shige shi a kowanne lokaci, da kowacce manufa, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna, su ne raka'o'i biyun gaisuwar masallaci.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

An so yin sallah raka'a biyu gaisuwa ga masallaci kafin zama.

Wannan umarni ne ga wanda ya yi nufin zama, wanda ya shiga masallaci ya fita kafin ya zauna umarnin bai shafe shi ba.

Idan mai sallah ya shiga (masallaci) alhali mutane suna cikin sallah, sai ya shiga cikinta tare da su, to, wannan ya wadatar masa daga raka'o'i biyun.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 96) (444).

Sahih Muslim (1/ 495) (714).

Kari (4)

المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (2/ 352).

فتح الباري لابن رجب (3/ 274).

التوضيح (5/524).

البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (15/ 287).