Skip to content

Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne

Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yace:

"Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".

«السِّوَاكُ مَطْهَرَةٌ لِلْفَمِ، مَرْضَاةٌ لِلرَّبِّ».

Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad.
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sanar damu cewa tsaftace hakora da itaciyar urak da makamancinta yana tsaftace baki daga datti da wari wadanda suke abin ki. Kuma cewa shi yana daga sabubban yardar Allah ga bawa; domin cewa a cikinsa akwai biyayya ga Allah da amsa umarninSa, da kuma abinda ke cikinsa na tsaftar da Allah - Madaukakin sarki - yake son ta.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Falalar asiwaki, da kwadaitarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga al'ummarsa da yawaitawa hakan.

Abinda yafi ga asiwaki shi ne yin amfani da itacan urak (kirya), yin amfani da makilin da burush yana tsayawa a madadinta.

Manazarta

Sunanu Nasa'i (1/ 10) (5).

Musnad Ahmad (40/ 240) (24203).

Kari (6)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (2/ 342).

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمصطفى الخِن وغيره (2/ 852).

تطريز رياض الصالحين.

لفيصل آل مبارك (ص675).