Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah
Daga baban Zubair ya ce:
Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.
كَانَ ابْنُ الزُّبَيْرِ يَقُولُ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ حِينَ يُسَلِّمُ: «لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الْفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ» وَقَالَ: «كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُهَلِّلُ بِهِنَّ دُبُرَ كُلِّ صَلَاةٍ».
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana HAILALA bayan ya sallame daga kowacce sallah ta farilla da wannan zikirin mai girma, Ma’anarsa ita ce: "Babu abin bautawa sai Allah"; Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. "Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya": Wato babu wanda yake tarayya da Shi a Allantaka [ cancantar bauta ] ko a rububiyya [ kasancewarSa Mahalicci, Mai azurtawa, Mai rayawa, Mai matarwa ] ko kuma a sunaye da siffofinSa. "Mulki na sa ne": Wato; Shi Ya ke da cikakken mulki wanda ya game komai, mulkin sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu. "Godiya ta sa ce": Wato shi ne wanda ya siffantu da cikakkiyar cika, wanda ake yabonSa da cika saboda so da girmawa a kowanne lokaci, na farin ciki da na damuwa. "Shi mai iko ne a kan komai": IkonSa cikakken iko ne ta kowacce fuska, babu abin da yake gagararsa, babu wani al’amari da zai gagare shi. "Ba dabara ba ƙarfi sai da yin Allah": Wato babu canji daga wani hali zuwa wani halin, ko daga saɓon Allah zuwa ga baiyayyarSa, haka babu ƙarfi, sai da Allah wanda Shi ne Mai taimako, kuma Wanda ake dogara da Shi. "Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi": karfafawa ce a kan ma’anar Allantaka da kuma kore shirka, da cewa babu wanda ya cancanci bauta in ba Shi ba. "Ni’ima ta Sa ce da falala": Shi ne wanda ya halicci ni’imomi kuma yake mallakarsu, yake kuma ba da su ga wanda Ya so cikin bayinSa. "Kyakkyawan yabo nasa ne": A bisa zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa da Ni’imominSa a kowanne lokaci. "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsantsanta addini a gareShi": Wato, muna masu Tauhidi, babu riya, kuma babu jiyarwa a kan biyayya ga Allah. "Koda kafirai sun ƙi": Wato muna masu tabbatuwa a kan Tauhidi da bauta masa ko da kafirai sun ƙi.
الثناء: تكرار المدح والذكر.
An so kulawada da wannan zikirin bayan kowacce sallah ta farilla.
Musulmi yana ji da addininsa, kuma yana bayyana ayyukan addininsa, ko da kafirai sun ƙi.
Idan a cikin Hadisi aka ce: "bayan sallah", to, idan abin da a ka ce a Hadisin zikiri ne, to, asali ana nufin bayan sallama, idan kuma addu’a ce, to, ana nufin kafin sallama.
Sahih Muslim (1/ 415) (594).
Kari (12)
سبل السلام شرح بلوغ المرام.
للصنعاني (1/ 293).
كنوز رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (17/ 61).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمصطفى الخِن وغيره (2/ 973).
بهجة الناظرين.
لسليم الهلالي (2/ 499).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.
لعلي القاري (2/ 762).
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (5/ 492).
An ambata a cikin littattafai
10 Littattafai- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلم«Babu abin bautawa da cancanta sai Allah Shi kaɗai Yake, ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya ma taSa ce, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Babu wata dabara babu wani ƙarfi face da (taimakon) Allah, babu abin bautawa da canc
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلمLã ilãha illallãh, wahdahu lã sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa alã kulli shai'in ƙadiir.
- YADDA SALLAR ANNABI - TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA AGARE SHI - TAKEكَيفِيَّةُ صَلَاةِ النَّبِيِّ ﷺ (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai Yake, ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya ma taSa ce, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Babu wata dabara babu wani ƙarfi face da (taimakon) Allah. Ya Allah babu mai hana abi
Kari (7)
- الذكر والدعاء والعلاج بالرقي من الكتاب والسنة"لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك، وله الحمد، وهو على كل شيء قدير. لا حول ولا قوة إلا بالله، لا إله إلا الله ولا نعبد إلا إياه، له النعمة وله الفضل، وله الثناء الحسن، لا إله إلا الله مخلصين له الدين ولو كره الكافرون".
- الذكر والدعاء والعلاج بالرقي من الكتاب والسنة"لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، آيبون، تائبون، عابدون، لربنا حامدون، صدق الله وعده، ونصر عبده، وهزم الأحزاب وحده" .
- العلم الواجب بدون فقه وبدون زيادات1لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ وَ
- تطبيق القرآن والأذكارأذكار الصباح والمساء((لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)) (مائةَ مرَّةٍ إذا أصبحَ)[30].
- رسالة في الأذكار1«لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ، وَلَهُ الحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ، وَلَه
- ما لا يسع أطفال المسلمين جهله«لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ و
- من الأحكام الفقهية في الطهارة والصلاة والجنائز«لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاَللَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَ