Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita
Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita", ta ce: Lokacin da Abu Salama ya rasu na ce: Waye a cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri? farkon gidan da ya yi hijra zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan sai na faɗeta (addu'ar), sai Allah Ya maye mini gurbinsa da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
«مَا مِنْ مُسْلِمٍ تُصِيبُهُ مُصِيبَةٌ فَيَقُولُ مَا أَمَرَهُ اللهُ: {إِنَّا لِلهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ} [البقرة: 156]، اللَّهُمَّ أْجُرْنِي فِي مُصِيبَتِي، وَأَخْلِفْ لِي خَيْرًا مِنْهَا، إِلَّا أَخْلَفَ اللهُ لَهُ خَيْرًا مِنْهَا»، قَالَتْ: فَلَمَّا مَاتَ أَبُو سَلَمَةَ قُلْتُ: أَيُّ الْمُسْلِمِينَ خَيْرٌ مِنْ أَبِي سَلَمَةَ؟ أَوَّلُ بَيْتٍ هَاجَرَ إِلَى رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم، ثُمَّ إِنِّي قُلْتُهَا، فَأَخْلَفَ اللهُ لِي رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم.
Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa ita ta ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa wata rana: Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi sai ya faɗi abinda Allah Ya so gare shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], (Ya Allah Ka bani lada) Ka bani ladan haƙurina (a cikin wannan musiba), ka canja mini (Ka maye mini gurbi) daga ita (da mafi alheri daga gareta); sai Allah Ya canja masa mafi alheri daga gareta. Ta ce : Lokacin da Abu Salama ya yasu na ce: Waye cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri?! farkon gidan da ya yi hijira zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan Allah Ya taimake ni sai na faɗeta, sai Allah Ya maye mini gurbin Abu Salama da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbta agare shi -.
Umarni da haƙuri a lokacin musibu da kuma rashin kururuwa.
Fuskantar da addu'a zuwa ga Allah a cikin musibu da suke sauka; domin canji yana gare shi (shi Allah).
Larurar mumini ya yi ruko da umarnin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda hikima bata bayyana daga umarninsa ba.
Alheri dukkansa yana cikin ruko da umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sahih Muslim (2/ 631) (918).
An ambata a cikin littattafai
5 Littattafai- ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARIالمنتقى من المتجر الرابح في ثواب العمل الصالح"Babu wani musulmin da musifa za ta same shi, sai ya faɗi abin da Allah Ya umarce shi: (Lallai mu ga Allah muke, kuma ga Allah za mu koma) Ya Allah Ka ba ni lada a cikin musiba ta, kuma Ka maye min gurbin ta da mafi alheri, sai Allah Ya may
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلم«Lallai mu daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma, Ya Allah Ka ba ni lada a musifata, Ka maye min mafi alkhairi daga gare ta»[197].
Kari (3)
- الذكر والدعاء والعلاج بالرقي من الكتاب والسنة"ما من مسلم تصيبه مصيبة فيقول ما أمره الله، إنا لله وإنا إليه راجعون. اللهم أجرني في مصيبتي، وأخلف لي خيراً منها إلا أخلف الله له خيراً منها" .
- فتاوى المرضىفتاوى المرضى «ما من مسلم تصيبه مصيبة، فيقول ما أمره الله: إنا لله وإنا إليه راجعون، اللهم أجرني في مصيبتي، وأخلف لي خيرًا منها. إلا أخلف الله له خيرا منها». قالت: فلما مات أبو سلمة، قلت: أي المسلمين خير من أبي سلمة؟ أول بيت هاجر إلى رسول الله صلى الله ع
- مجموعة زاد التربية الإسلامية (2)1«مَا مِنْ مُسْلِمٍ تُصِيبُهُ مُصِيبَةٌ فَيَقُولُ مَا أَمَرَهُ ﷲ: إِنَّا ﷲ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ، اللَّهُمَّ أْجُرْنِي فِي مُصِيبَتِي، وَأَخْلِفْ لِي خَيْرًا مِنْهَا؛ إِلَّا أَخْلَفَ ﷲ لَهُ خَيْرًا مِنْهَا». قالت: «فلما مات أبو سلمة ق