Skip to content

Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu

Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.

«لَا تَجْلِسُوا عَلَى الْقُبُورِ، وَلَا تُصَلُّوا إِلَيْهَا».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zama a kan kaburbura. Kamar yadda ya hana yin Sallah ana kallon kaburbura, ta yadda kabari zai kasance ta inda alƙiblar mai Sallah take, domin hakan hanya ce ta shirka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Hana yin sallah a maƙabartu, ko tsakanin kaburbura, ko ana kallon kaburbura, sai dai Sallar janaza kamar yadda hakan ya tabbata a Sunnah.

Hana yin Sallah ana kallon kaburbura don toshe ƙofar kaiwa ga shirka.

Musulunci ya hana wuce iyaka a kan kaburbura ya kuma hana wulaƙantasu, ba wuce iyaka, kuma ba wulaƙantawa.

Alfarmar Musulmi tana nan bayan rasuwarsa, saboda faɗin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Karya ƙashin mamaci kamar karya shi yana raye ne.

Manazarta

Sahih Muslim (2/ 668) (972).

Kari (6)

توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (2/ 30).

فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام.

لمحمد العثيمين (1/ 522).

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (4/ 285).