Skip to content

Mafi cancantar sharuɗɗa da za ku cika; su ne wadanda aka halatta muku mata da su

Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Mafi cancantar sharuɗɗa da za ku cika; su ne wadanda aka halatta muku mata da su.

«أَحَقُّ الشُّرُوطِ أَنْ تُوفُوا بِهِ مَا اسْتَحْلَلْتُمْ بِهِ الْفُرُوجَ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa mafi cancantar sharaɗin da za a cika shi ne wanda ya kasance dalili na halatta jin daɗi da mace, su ne sharuɗɗan da suke na halal ga mace ta nema a lokacin ɗaurin aure.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Wajibcin cika sharuɗɗa wanda ɗayan ma’aurata ya sa, sai dai sharaɗin da ya haramta halal, ko ya halatta haram.

Cika sharuɗɗan aure ya fi sauran ƙarfi, domin yana matsayin halatta farji ne.

Girman matsayin aure a Musulunci ta yadda ya fi kowanne sharaɗi ƙarfin cikawa.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (3/ 190) (2721).

Sahih Muslim (2/ 1035) (1418).

Kari (4)

الإلمام بشرح عمدة الأحكام.

لإسماعيل الأنصاري (2/ 63).

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

لعبد الله البسام (ص573).