Skip to content

Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama

Daga Mu'awiya -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:

"Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".

«الْمُؤَذِّنُونَ أَطْوَلُ النَّاسِ أَعْنَاقًا يَوْمَ الْقِيَامَةِ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ladanai waɗanda suke kiran sallah sune mafiya tsawon wuyaye a cikin mutane ranar alƙiyama, saboda girman aikinsu, da kuma yawan alherinsu, da girman ladansu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Falalar kiran sallah da kwaɗaitarwa a cikinsa.

Bayanin matsayin ladanai da ɗaukakar matsayinsu a ranar alƙiyama.

Manazarta

Sahih Muslim (1/ 290) (387).

Kari (8)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (2/ 251).

شرح رياض الصالحين.

لابن عثيمين (5/ 31).

شرح صحيح مسلم.

النووي (4/ 89).

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (1/ 768).