Masu tsanantawa sun halaka
Daga Abdullahi Dan Mas'ud ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Masu tsanantawa sun halaka" ya fadi hakan ne har sau uku.
«هلك المُتَنَطِّعُون» قالها ثلاثًا.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da tabewar masu tsanantawa - ba tare da shiriya da ilimi ba - a addinin su da duniyar su, da kuma maganganun su da ayyuakan su, masu ketare iyakar shari'a da su wanda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi.
....:
Haramcin tsanantawa da dorawa kai abinda ba zai iyaba a cikin al'amura gaba dayan su, da kwadaitarwa akan nisantarhakan a kowane abu; musammanma a cikin ibadu da girmama salihai.
Neman mafi cika a cikin ibadu da wasunsu al'amari ne abin yabo; kuma yana kasancewane ta hanyar bin shari'a.
Son karfafa al'amari mai muhimmanci; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya maimaita wannan jumlar har sau uku.
Martabar musulunci da kuma saukinsa.
Sahih Muslim (4/ 2055) (2670).
Kari (4)
الجديد في شرح كتاب التوحيد.
للقرعاوي (ص180).
الملخص في شرح كتاب التوحيد.
لصالح الفوزان (ص167).
An ambata a cikin littattafai
4 LittattafaiKari (4)
- حراسة التوحيدإقامة البراهين على حكم من استغاث بغير الله«هَلَكَ المُتَنَطِّعُونَ» قَالَهَا ثَلَاثًا.
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 1 «هَلَكَ الْمُتَنَطِّعُونَ» قَالَهَا ثَلاَثاً.
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 8«هَلَكَ المُتَنَطِّعُونَ» قَالَهَا ثَلاثاً.
- مجموعة زاد الحديث(2)1«هلك المتنطعون - قالها ثلاثا»