Skip to content

Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama

Daga Abu Al-darda - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gatreshi - ya ce:

"Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama".

«مَنْ رَدَّ عَنْ عِرْضِ أَخِيهِ رَدَّ اللهُ عَنْ وَجْهِهِ النَّارَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».

Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa musulmi a bayan idonsa ta hanyar hana zarginsa ko munana masa, to, lallai Allah Zai kareshi daga azaba a ranar al-ƙiyama.

Ma"anonin Kalmomi

عِرْضِ أَخِيهِ: العرض هو ما يُمْدَح به الإنسان أو يذم.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Hani daga magana a kan mutuncin musulmai.

Sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki, wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kareshi daga wuta.

Musulunci addinin 'yan uwantaka ne da taimakekeniya a tsakanin ma'abotansa.

Manazarta

Sunan Tirmizi (3/ 488) (1931).

Musnad Ahmad (45/ 528) (27543).

Kari (8)

توضيح الأحكام من بلوغ المرام.

للبسام (7/ 499).

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (10/ 349).

فتح ذي الجلال والإكرام.

لابن عثيمين (6/ 437).

سبل السلام بشرح بلوغ المرام.

للصنعاني (2/ 692).