7 : 133
فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلۡجَرَادَ وَٱلۡقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَٰتٖ مُّفَصَّلَٰتٖ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ
Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.
Explanation & meanings · 1
- Ãyõyin da suka je musu a cikin lõkatai daban-daban dõmin a ja hankalinsu, kõ zã su yi ĩmãni. Kõwace ãyã tanã kwãna bakwai sunã wahala da ita, sa'an nan su rõƙi Mũsã ya yi addu'a a kuranye ta, sa'an nan a bãyan wani lõkaci sai su kõma wa kãfircinsu, kamar yadda ãyõyi mãsu biyar wannan suka bayyana.