62 : 3
وَءَاخَرِينَ مِنۡهُمۡ لَمَّا يَلۡحَقُواْ بِهِمۡۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Da waɗansu mutãne daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
Explanation & meanings · 1
- Su ne Ajamãwan da zã su musulunta su bi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kõ kuwa duk wanda ya musulunta a bãyan sahabban Annabi. Wannan yanã nunã falalar sahabbai a kan waɗansunsu.