Skip to content
النِّسَاء /

Aya 109

4 : 109

Aya 109 of النِّسَاء (4 : 109). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 109

هَٰٓأَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ جَٰدَلۡتُمۡ عَنۡهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فَمَن يُجَٰدِلُ ٱللَّهَ عَنۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا

Gã ku, yã waɗannan! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?

Explanation & meanings · 1
  1. Wannan yana nũna aikin lauya (Lawyer) dõmin ya taimaki marasa gaskiya sabõda ya kuɓuta harãmun ne, har dai idan zã a mayar da laifi ga wani barrantacce ko kuwa za a karɓe hakkin mai hakki a bai wa wanda bai cancanta da shi ba. Amma wakĩlin sharĩ'a yana halatta idan bai zama dõmin ɓõye gaskiya ba. Wakĩlai irin na zãmanin nan mãsu sanã'a da wannan, sũ ne karnukan dũniya na farautar haram dõmin su sha jini.