Skip to content
آل عِمران /

Aya 73

3 : 73

Aya 73 of آل عِمران (3 : 73). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

آل عِمران Ayoyi 200
3 : 73

وَلَا تُؤۡمِنُوٓاْ إِلَّا لِمَن تَبِعَ دِينَكُمۡ قُلۡ إِنَّ ٱلۡهُدَىٰ هُدَى ٱللَّهِ أَن يُؤۡتَىٰٓ أَحَدٞ مِّثۡلَ مَآ أُوتِيتُمۡ أَوۡ يُحَآجُّوكُمۡ عِندَ رَبِّكُمۡۗ قُلۡ إِنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

"Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani."

Explanation & meanings · 1
  1. Maganganu sun shiga jũna dõmin a yi raddin kõwace guntuwar magana da jawãbin da ya dãce da ita tãre da ita. A lũra da kyau.