Skip to content
القَصَص /

Aya 38

28 : 38

Aya 38 of القَصَص (28 : 38). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

القَصَص Ayoyi 88
28 : 38

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ مَا عَلِمۡتُ لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرِي فَأَوۡقِدۡ لِي يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجۡعَل لِّي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."

Explanation & meanings · 1
  1. Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cewa ajurru, aka gina masa dõgon bene, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: "yã kashe Ubangijin Mũsa." Bayan haka sai benen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cewar Fir'auna, "Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata," ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnewa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma.