Skip to content
الأنبيَاء /

Aya 92

21 : 92
الأنبيَاء Ayoyi 112
21 : 92

إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

Lalle ne wannan ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.

Explanation & meanings · 1
  1. Al'ummar Musulmi duka guda ce kõ da yake Annabãwansu sun zo dabam-dabam, a cikin lõkuta mãsu nĩSa tsakãninsu da harsuna dabam-dabam dõmin duk aƙĩdarsu guda ce a kan Ubangiji guda ne. Sa'an nan daga bãya waɗanda suka fita daga wannan aƙĩdar suka rarrabu ƙungiya-ƙungiya.