Skip to content
طه /

Aya 87

20 : 87

Aya 87 of طه (20 : 87). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

طه Ayoyi 135
Sura · طه
Hausa · Gummi
20 : 87

قَالُواْ مَآ أَخۡلَفۡنَا مَوۡعِدَكَ بِمَلۡكِنَا وَلَٰكِنَّا حُمِّلۡنَآ أَوۡزَارٗا مِّن زِينَةِ ٱلۡقَوۡمِ فَقَذَفۡنَٰهَا فَكَذَٰلِكَ أَلۡقَى ٱلسَّامِرِيُّ

Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa."

Explanation & meanings · 1
  1. Alõkacin da Banĩ Isrã'ĩla zãsu fita daga Masar sun yi aron mundãyen mutãnen Masar dõmin su nũna cewa biki suke yi, bã gudu zã su yi ba, dõmin kada a bĩ su da wuri waɗannan mundãyen ne sãmiri ya tãra a bãyan tafiyar Mũsã zuwa ga Mĩƙãtin Ubangijinsa ya ƙera musu maraƙi mai jiki irin na mutãne da sauti irin na shãnu dõmin yã yi masa magudãnar iska a cikin cikinsa idan iskar ta fito, sai a jĩ ta da sauti kamar sautin kũkan shãnu. Kuma shi maraƙin bã ya dã wani rai, bã ya mõtsi, sai dai ƙũgin kawai.