12 : 97
قَالُواْ يَٰٓأَبَانَا ٱسۡتَغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَآ إِنَّا كُنَّا خَٰطِـِٔينَ
Suka ce: "Yã ubanmu! ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure."
Explanation & meanings · 1
- Ɗiyan Yãƙũbu sunã iƙrãri da laifinsu, sunã neman Allah Ya gãfarta musu gaba ɗaya. Ubansu yanã jinkirta nema musu gãfara gun Allah har a lõkacin asuba kõ kuwa daren Jumma'a dõmin ya yi rõƙo a lõkacin karɓar addu'a. Wannan yã nũna anã iya neman mai albarka kõ wani mutum yayi wa wani mutum Addu'a.