12 : 94
وَلَمَّا فَصَلَتِ ٱلۡعِيرُ قَالَ أَبُوهُمۡ إِنِّي لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَۖ لَوۡلَآ أَن تُفَنِّدُونِ
Kuma, a lõkacin da ãyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba."
Explanation & meanings · 1
- Yãƙũba da jĩkõkinsa. Yanã gaya musu, cewa yanã shãƙar ƙanshin Yũsufu, su kuma suna jingina shi ga ruɗewar tsũfa dõmin rabonsa da Yũsufu shħkara talãtin da biyar zuwa Arba'in.