Skip to content
يُونس /

Aya 72

10 : 72
يُونس Ayoyi 109
Sura · يُونس
Hausa · Gummi
10 : 72

فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَمَا سَأَلۡتُكُم مِّنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۖ وَأُمِرۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

"Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."

Explanation & meanings · 1
  1. Watau dukan abin da na zo muku da shi na umurni kõ hani, to, ni ma an umurce ni da yinsa kõ barinsa. Kuma bã ni neman wata ijãrar karantarwa daga gare ku dõmin Allah Ya umarce ni da iyar da manzancinsa zuwa gare ku, sabõda haka Shi ne zai biyã ni tsãdar aikĩna.