Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

63 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce, kuma ita faƙo ce kuma dashenta (shi ne): Subhanallah, (tsarki ya tabbata ga Allah), Alhamdulillah (godiya ta tabbata ga Allah), Lailaha Illallahu, (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)".
Hasan ne a baki dayan Riwayoyin sa Tirmizi ne ya ruwaito shi
"Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya".
Hasan ne da wani Sanadin Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskarSa Mai girma, da sarautarSa daɗaɗɗiya, daga Shaiɗan abin jefewa", Ya ce: Wannan kawai? na ce: Eh, ya ce: Idan ya ce haka Shaiɗan zai ce : an kiyaye shi daga gareni ragowar yinin.
Hasan ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
"ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".
Hasan ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
"Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki".
Hasan ne da wani Sanadin Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».
Hasan ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
«Yana daga kyan Musuluncin mutum yabar abin da babu ruwansa».
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Tirmizi da Ahmad ne sun rawaito shi
«Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su».
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Dar Al-Kutni ya ruwaito shi a cikin Sunan din sa da waninsa