Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

79 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
«Babu cuta ba cutarwa».
Hasan ne Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin Musnad.
Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.
Ingantacce ne Ibnu Majah ne ya ruwaito shi
"Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe alhariri da hagunsa, kuma zinare da damansa, sannan ya ɗaga hannayensa da su, sai ya ce: "Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu".
Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi
"Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
«‌Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi