Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

38 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
"Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?" Suka ce: Eh, ya ce: "Yin sulhu tsakanin waɗanda ke rigima, domin ɓacin tsakanin waɗanda ke rigima shine mai askewa".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shi
Wasu mutane biyu sun bani labarin cewa sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Hajjin ban kwana alhali shi yana raba sadaka (zakka), sai suka tambaye shi zakkar, sai ya ɗaga idanuwansa garemu ya kuma yi ƙasa da su, sai ya ganmu ƙarfafa ne, sai ya ce: «Idan kun so zan baku ita, babu rabo a cikinta ga mawadaci, ko ƙaƙƙarfan da yake iya neman na kansa».
Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i ne suka ruwaito shi.
«Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne».
Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i ne suka ruwaito shi.
Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce.
Hasan ne ta jimillar hanyoyinsa Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi
Na zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son (shiga) Musulunci, sai ya umarceni da in yi wanka da ruwa da magarya.
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
"Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
"ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".
Hasan ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi