Skip to content

Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa

Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

"Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".

«إِذَا أَحَبَّ الرَّجُلُ أَخَاهُ فَلْيُخْبِرْهُ أَنَّهُ يُحِبُّهُ».

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi.
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana daya daga sabubban da suke karfafa alaka tsakanin muminai kuma suke yada soyayya a tsakaninsu, shi ne cewa idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana son sa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Falalar tsarkakakkiyar soyayya saboda Allah - Madaukakin sarki - ba dan maslaha ta duniya ba.

Anso sanadar da wanda ake so sabo da Allah da soyayyrsa, dan soyayya da kauna su karu.

Yada soyayya tsakanin muminai yana karfafa 'yan uwantaka ta imani, kuma yana kiyaye zamantakewa daga rarrabuwa.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (7/ 444) (5124).

Sunan Tirmizi (4/ 199) (2392).

Sunanul Kubura Na Nasa'i (9/ 87) (9963).

Musnad Ahmad (28/ 408) (17171).

Kari (12)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (1/ 450).

تطريز رياض الصالحين.

لفيصل المبارك (ص258).

رياض الصالحين للنووي.

(ص138) (383).

سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها.

للألباني (1/ 777).

فيض القدير شرح الجامع الصغير.

للمناوي (1/ 247).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (6/ 279).