Skip to content

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.

كان النبي صلى الله عليه وسلم يقول بين السجدتين: «اللَّهمَّ اغْفِرْ لي، وارْحَمْنِي، وعافِني، واهْدِني، وارزقْنِي».

Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Hasan ne a baki dayan Riwayoyin sa
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Shar’antuwar wannan Addu’ar a zaman dake tsakanin sujjada biyu.

Falalar wannan Addu’ar saboda abin da ta ƙunsa na alheran duniya da lahira.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (2/ 138) (850).

Sunan Tirmizi (1/ 317) (284).

Sunanu Ibn Majah (2/ 64) (898).

Musnad Ahmad (5/ 72) (2895).

Kari (6)

مشكاة المصابيح.

للتبريزي (1/ 283).

سبل السلام شرح بلوغ المرام.

لمحمد الصنعاني (1/ 274).

توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (2/ 240).