Skip to content

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son Addu'ar da ta tattaro komai, kuma yana ƙyale wacce ba ita ba

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son Addu'ar da ta tattaro komai, kuma yana ƙyale wacce ba ita ba.

كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسْتَحِبُّ الْجَوَامِعَ مِنَ الدُّعَاءِ، وَيَدَعُ مَا سِوَى ذَلِكَ.

Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son addu'o'i masu tattaro alherin duniya da lahira wacce lafazinta kaɗan ne kuma ma'anarta yana da yawa, kuma a cikinta akwai yabo ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da manufofi na gari, kuma yana barin koma bayan haka.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

An so addu'a da lafuza sassauƙa masu tattaro ma'anonin alheri, da kuma ƙin ɗorawa kai wahala da tsananatawa a cikin mas'ala, hakan saɓanin karantarwar Annabi ce - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

An keɓanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kalmomi masu tattaro (ma'anoni).

Kwaɗayi akan abinda ya tabbata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da shi; koda ya kasance mai tsawo ne, kuma kalmominsa sun yi yawa, dukkansa daga addu'o'i ne masu tattarowa.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (2/ 605) (1482).

Musnad Ahmad (42/ 76) (25151).

Kari (8)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (2/ 542).

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (2/ 1003).

شرح رياض الصالحين.

لابن عثيمين (6/ 15).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (17/ 349).