Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".
«مَنْ عَادَ مَرِيضًا، لَمْ يَحْضُرْ أَجَلُهُ فَقَالَ عِنْدَهُ سَبْعَ مِرَارٍ: أَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ، إِلَّا عَافَاهُ اللَّهُ مِنْ ذَلِكَ الْمَرَضِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani musulmin da zai ziyarci wani musulmi a cikin rashin lafiyarsa wanda lokacin mutuwarsa bai yi ba, sannan mai ziyarar ya yi wa mara lafiya addu'a da faɗinsa: (Ina roƙon Allah Mai girma) a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, (Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya), kuma ya maimaitata hakan sau bakwai sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar.
An so addu'a ga mara lafiya da wannan addu'ar, da kuma maimaitata sau bakwai.
Tabbatar da waraka ga wanda aka faɗi wannan addu'ar a wurinsa da izinin Allah - Maɗaukakin sarki -, in ta bijiro da gaskiya da kuma salaha.
Zai faɗi wannan addu'ar ne a ɓoye da bayyane, dukkan hakan ya halatta, sai dai idan ya jiyar da mara lafiyar to shi ya fi; domin a cikinsa akwai shigar da farin ciki gare shi.
Sunan Abi Dawud (5/ 22) (3106).
Sunan Tirmizi (3/ 593) (2083).
Sunanul Kubura Na Nasa'i (9/ 385) (10820).
Musnad Ahmad (4/ 40) (2137).
Kari (10)
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (2/ 163).
تطريز رياض الصالحين.
لفيصل آل مبارك (ص537).
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (4/ 483).
كنوز رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (11/ 559).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (1/ 689).
An ambata a cikin littattafai
5 Littattafai- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلم«Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya»
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلمAs'alullāhal azīma, rabbal arshil azīmi, an yashfiyak.
Kari (3)
- الذكر والدعاء والعلاج بالرقي من الكتاب والسنة"من عاد مريضاً لم يحضر أجله فقال عنده سبع مرات: أسأل الله العظيم رب العرش العظيم أن يشفيك، إلَّا عافاه الله من ذلك المرض" .
- تطبيق القرآن والأذكارالرقية الشرعيةأَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ رَبَّ العَرْشِ العَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ (سبع مرات)[2].
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 5«مَنْ عَادَ مريضاً لَمْ يَحْضُرْهُ أجَلُهُ، فَقَالَ عندهُ سبعَ مَرَّات: أسألُ اللهَ العَظيم ربَّ العرشِ العظيمِ أنْ يَشْفيَكَ، إلَّا عَافاه اللهُ من ذلك المرض».