Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".
«إِنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإِنَّ اللهَ مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاءَ، فَإِنَّ أَوَّلَ فِتْنَةِ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَانَتْ فِي النِّسَاءِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa duniya mai zakice a abubuwan zaki, kuma koriya a abin gani, sai mutum ya rudu da ita ya yi zari a cikinta ya kuma sanya ta mafi girman himmarsa. Kuma cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ya sanya shashinmu zai maye gurbin sashi a wannan duniyar, dan ya duba ya zamu yi aiki, shin zamu tsaya da biyayyarSa, ko zamu saba maSa? Sannan ya ce: Ku kiyayi jin dadin duniya ya rudeku da kawarta, sai ya doraku akan barin abinda Allah Ya umarceku da shi, da kuma afkawa a cikin abinda ya haneku daga gareshi. Daga mafi girman abinda ya wajaba a kiyaya daga gare shi daga fitintinun duniya (su ne) mata, cewa ita ce farkon fitinar da Banu Isra'ila suka afka a cikinta.
خَضِرَة: غضة ناعمة طرية. فالدنيا تُشبِه في الميل إليها الفاكهة الحلوة الطرية في مذاقها، الخضرة في لونها.
Kwadaitarwa akan lazimtar tsoron Allah, da barin shagaltuwa da zahirin duniya da kawarta.
Kiyayewa daga fitinuwa da mata, na kallo ko sakaci da cakuduwarsu da maza manisanta, ko wanin hakan.
Fitinar mata tana daga mafi girman fitintinu a duniya.
Wa'azantuwa da daukar izina daga al'ummun da suka gabata, abinda ya faru ga Banu isra'ila zai iya faruwa ga wasunsu.
Fitinar mata idan ta kasance mata ce to ita zata iya dorawa mutum ciyarwar da ba zai iya ba, sai ta shagaltar da shi daga neman al'amuran Addini, ta kuma dora masa halaka a neman duniya, idan kuma manisanciya ce to fitinarta da rudar da maza ne da karkatar dasu daga gaskiya idan sun fita sun cakuda dasu, musanmama dai idan sun zama matsiraita masu shiga ta nuna tsiraici, wannan zai iya kaiwa zuwa afkawa a cikin zina a girmansa, to yana kamata ga mumini ya yi riko ga Allah, da kuma kwadayi gareShi don kubuta daga fitinarsu.
Sahih Muslim (4/ 2098) (2742).
Kari (6)
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (1/ 146).
كنوز رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (2/ 173).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (1/ 103).
An ambata a cikin littattafai
5 LittattafaiKari (5)
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 1 «إنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإنَّ الله مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاء، فَإنَّ أوَّلَ فِتنَةِ بَنِي إسْرَائيلَ كَانَتْ في النِّسَاءِ».
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 3«إنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإنَّ اللهَ تَعالىٰ مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاءَ».
- مجموعة زاد التربية الإسلامية (4)التربية الإسلامية 4«إِنَّ الدُّنْيا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإِنَّ الله مُسْتَخْلِفُكُمْ فيها، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فاتَّقُوا الدُّنْيا، واتَّقُوا النِّساءَ، فَإِنَّ أَوَّلَ فِتْنَةِ بَنِي إِسْرائِيلَ كانَتْ في النِّساءِ».
- مجموعة زاد الحديث(2)1«إِنَّ الدُّنْيَا حُلْوَةٌ خَضِرَةٌ، وَإِنَّ الله مُسْتَخْلِفُكُمْ فِيهَا، فَيَنْظُرُ كَيْفَ تَعْمَلُونَ، فَاتَّقُوا الدُّنْيَا وَاتَّقُوا النِّسَاءَ، فَإِنَّ أَوَّلَ فِتْنَةِ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَانَتْ فِي النِّسَاءِ»
- مجموعة زاد الحديث(2)1«فان أوَّلَ فتنةِ بني إسرائيل كانت في النساء»