Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".
«إِذَا قَالَ الْمُؤَذِّنُ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، فَقَالَ أَحَدُكُمُ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، ثُمَّ قَالَ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، ثُمَّ قَالَ: أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، قَالَ: أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ، قَالَ: لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، ثُمَّ قَالَ: حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، قَالَ: لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، ثُمَّ قَالَ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، قَالَ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، ثُمَّ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مِنْ قَلْبِهِ دَخَلَ الْجَنَّةَ».
Kiran sallah shi ne sanar da mutane shigowar lokacin sallah, kuma kalmomin kiran sallah kalmomi ne masu tattaro aƙidar imani. A wannan Hadisin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana abin da aka shara'anta a yayin jin kiran sallah, shi ne mai ji ya faɗi irin abin da ladanin yake faɗa, idan ladani ya ce: "Allah ne mafi girma", mai ji ya ce: "Allah ne mafi girma", haka nan; sai dai a lokacin fadin ladani: "Ku yi gaggawa zuwa sallah", "Ku yi gaggawa zuwa tsira" sai mai ji ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah". Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa wanda ya maimaita tare da ladani yana mai tsarkake (niyya) daga zuciyarsa zai shiga aljanna. Ma'anonin kalmar kiran sallah: "Allah ne mafi girma": Wato cewa Shi (Allah) - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi girma mafi ɗaukaka mafi girma daga dukkan komai. "Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne": Wato ina tabbatarwa kuma ina shaidawa da harshena da zuciyata cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, Allah - Mai girma da ɗaukaka -Ya aiko shi , kuma yana wajaba a yi masa biyayya . "Ku yi gaggawa zuwa sallah", wato ku zo zuwa sallah, da faɗin mai ji: "Babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah", wato babu dabara a kuɓuta daga abubuwan da suke hana biyayya, babu ƙarfi a kan aikatasu, kuma babu iko a kan kowanne abu daga abubuwa sai dace daga Allah - Maɗaukakin sarki -. "Ku yi gaggawa zuwa tsira", wato ku zo zuwa sababin tsira, shi ne rabauta da aljanna da tsira daga wuta.
...:
Falalar amsawa ladani da irin abin da yake faɗa sai dai a Hai'ala biyu kawai, sai ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah".
Sahih Muslim (1/ 289) (385).
Kari (3)
إكمال المعلم (2/253).
شرح النووي على مسلم (4/88).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (9/ 116).
An ambata a cikin littattafai
3 Littattafai- TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI«Idan mai kiran sallah ya ce: Allahu Akbar Allahu Akbar, sai ɗayanku ya ce: Allahu Akbar Allahu Akbar, sannan ya ce: Ash'hadu alla ilaha illallahu, kuma shima ya ce: Ash'hadu alla ilaha illallahu, sannan ya ce: Ash'hadu anna Muhammadan rasu
- ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARIالمنتقى من المتجر الرابح في ثواب العمل الصالح"Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ɗayan ku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan yace: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yace: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai