Skip to content

Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah

Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.

سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ العَمَلِ أَحَبُّ إِلَى اللَّهِ؟ قَالَ: «الصَّلاَةُ عَلَى وَقْتِهَا»، قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ بِرُّ الوَالِدَيْنِ» قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ» قَالَ: حَدَّثَنِي بِهِنَّ، وَلَوِ اسْتَزَدْتُهُ لَزَادَنِي.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.

Ma"anonin Kalmomi

.....:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Fifikon ayyuka a tsakaninsu gwargwadon yadda Allah yake son su .

Kwadaitarwar muslmi akan kwadayi akan ayyuka mafifita sai mafifita.

Fifikon amsawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafifitan ayyuka gwargwadan sabanin mutane da halayensu, da abinda yake mafi yawan amfani ga kowanne daya daga cikinsu.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 112) (527).

Sahih Muslim (1/ 90) (85).

Kari (6)

الإلمام بشرح عمدة الأحكام.

لإسماعيل الأنصاري (1/ 70).

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

للبسام (ص84).

تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام.

لابن عثيمين (1/ 108).