Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".
«البَسُوا مِنْ ثِيَابِكُمُ البَيَاضَ، فَإِنَّهَا مِنْ خَيْرِ ثِيَابِكُمْ، وَكَفِّنُوا فِيهَا مَوْتَاكُمْ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryar da maza cewa su sa tafafi masu farin launi da kuma yi wa mamata likkafani a cikinsu; domin cewa sune mafi alherin tufafi.
An so sanya farin tufafi, kuma waninsa na wata kalar ma yana halatta.
An so yi wa mamata likkafani da fararen (tufafi).
Shaukani ya ce: Hadisin yana nuni akan halaccin sanya fari da yi wa mamata likkafani da shi; kasancewarsa ya fi waninsa tsarkaka, amma kasancewarsa ya fi tsarki to wannan zahiri ne, amma kasancewarsa ya fi tsafta domin cewa mafi ƙanƙatar abu idan ya faɗa kansa zai bayyana sai ya fifita.
Sunan Abi Dawud (6/ 27) (3878).
Sunan Tirmizi (2/ 311) (994).
Sunanu Ibn Majah (2/ 453) (1472).
Kari (1)
ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (19/ 16).