Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce :
«Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
«إِنَّ أَدْنَى مَقْعَدِ أَحَدِكُمْ مِنَ الْجَنَّةِ أَنْ يَقُولَ لَهُ: تَمَنَّ فَيَتَمَنَّى، وَيَتَمَنَّى، فَيَقُولُ لَهُ: هَلْ تَمَنَّيْتَ؟ فَيَقُولُ: نَعَمْ، فَيَقُولُ لَهُ: فَإِنَّ لَكَ مَا تَمَنَّيْتَ وَمِثْلَهُ مَعَهُ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi ƙanƙantar matsayi da daraja ga wanda ya shiga aljanna shi ne Ya ce da shi: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, har sai ya zama babu wani burin da zai rage masa sai ya ambace shi , sai Ya ce masa: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce masa: To lallai kana da abinda ka yi burin dama kwatankwacinsa tare da shi.
Fifikon matsayin 'yan aljanna.
Bayanin girman karamcin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
Ni'imar aljanna ba ta taƙaituwa akan wani ayyanannen abu, kai mumini zai samu dukkan abinda yake burinsa kuma ransa yake sha'awarsa dan falala da kyauta da kuma karamci daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Sahih Muslim (1/ 167) (182).
Kari (8)
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.
لعلي القاري (9/ 3585).
تطريز رياض الصالحين.
لفيصل آل مبارك (ص1090).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (3/ 348).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (2/ 1292).