Skip to content

Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba".

«رَغِمَ أَنْفُ، ثُمَّ رَغِمَ أَنْفُ، ثُمَّ رَغِمَ أَنْفُ»، قِيلَ: مَنْ؟ يَا رَسُولَ اللهِ قَالَ: «مَنْ أَدْرَكَ أَبَوَيْهِ عِنْدَ الْكِبَرِ، أَحَدَهُمَا أَوْ كِلَيْهِمَا فَلَمْ يَدْخُلِ الْجَنَّةَ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ƙasƙanci da taɓewa har saida hakan ya kai, kai ka ce ya ɗora hancinsa a cikin ƙasa - ya maimaitata sau uku - sai aka tambaye shi: Waye wannan ya manzon Allah wanda ka yi mummunar Addu’a akansa? Sai (Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata aagre shi - ya ce: Wanda ya riski mahaifansa a lokacin tsufa - ɗayansu ko su biyun -, ba su zama sababi na shigarsa aljanna ba; hakan saboda rashin kyautata musu da kuma saɓa musu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Wajabcin biyayya ga mahaifa, kuma hakan yana daga sabubban shiga aljanna, musamman ma a lokacin tsufansu da rauninsu.

Saɓawa iyaye yana daga manyan zunubai.

Manazarta

Sahih Muslim (4/ 1978) (2551).

(16/ 108).

Kari (7)

بهجة الناظرين.

لسليم الهلالي (1/ 394).

نزهة المتقين.

لمجموعة من الباحثين (1/ 308).

فيض القدير شرح الجامع الصغير.

زين الدين المناوي (4/ 34).

شرح النووي على مسلم.