Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِلْأَشَجِّ أَشَجِّ عَبْدِ الْقَيْسِ: «إِنَّ فِيكَ خَصْلَتَيْنِ يُحِبُّهُمَا اللهُ: الْحِلْمُ، وَالْأَنَاةُ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Munzir ibnu A'iz ga mai tabo a fuskar nan na ƙabilar Abdulƙais kuma shugabanta - Allah Ya yarda da shi - Lallai kai kana da siffofi biyu Allah Yana sonsu, sune: Hankali, da kuma tabbata da nutsuwa da kuma rashin gaggawa.
Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da haƙuri da kuma dangana.
Kwaɗaitarwa akan tabbata a cikin al'amura da kuma duba ƙarshensu.
Haƙuri da dangana suna daga cikin siffofi ababen yabo.
Mutum ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - akan abinda Ya halicce shi akansa na ɗabi'u ababen yabo.
Kalmar al-Ashaj ita ce wanda aka jiwa rauni a fuska, ko a kai, ko goshi.
Sahih Muslim (1/ 48) (17).
Kari (6)
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (1/ 681).
تطرز رياض الصالحين.
لفيصل آل مبارك (ص414).
المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج.
للنووي (1/ 189).