Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna
Daga Abu Sa'idu Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna".
«الحَسَن والحُسَيْن سَيِّدا شَباب أهْل الجنة».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa jikokinsa biyu Alhassan da Alhussain 'ya'yan Ali ɗan Abu Ɗalib da Faɗima 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma Allah Ya yarda da su -, su ne shugabannin wanda ya mutu a falala alhali shi yana saurayi kuma ya shiga aljanna, ko cewa sune shugabannin matasan 'yan aljanna in an cere Annabawa da Khalifofi Masu shiryarwa.
A cikinsa akwai falala ta zahiri ga Hassan da Hussain - Allah Ya yarda da su -.
An ce a cikin ma'anar hadisin: Cewa su a lokacin hadisin sune shugabannin waɗanda sune daga 'yan aljanna cikin matasan wannan zamanin, ko kuma cewa sune mafifita daga waɗanda falala mai gamewa ba ta tabbata a cikinsa ba kamar Annabawa da Khalifofi, ko kuma cewa sune shugabannin waɗanda suka siffantu da siffofin samartaka da yarinta kamar karamci da gwarzantaka, kuma bai zo da shekarun matasa da hakan ba; domin Hassan da Hussain sun mutu alhali suna gwaraza.
Sunan Tirmizi (6/ 113) (3768).
Musnad Ahmad (17/ 31) (10999).
Kari (6)
حاشية السندي على سنن ابن ماجه.
محمد بن عبد الهادي التتوي (1/ 56).
تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي.
محمد المباركفوري (10/ 178).
المصباح المنير في غريب الشرح الكبير.
لأحمد الفيومي (1/ 294).
An ambata a cikin littattafai
3 LittattafaiKari (3)
- المعايشون للمصطفى صلى الله عليه وسلم(الحسن والحسين سيِّدا شباب أهل الجنة)). ([291])
- المعايشون للمصطفى صلى الله عليه وسلم(الحسن والحسين سيدا شباب أهل الجنة))،([325])
- المناهج التعليمية - الصف السادسالمناهج الدراسية - التوحيد - الصف السادس «الْحَسَنُ وَالْحُسَيْنُ سَيِّدَا شَبَابِ أَهْلِ الْجَنَّةِ»[38].