Skip to content

Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".

«اللهم لا تجعل قبري وثنًا، لعن الله قومًا اتخذوا قبور أنبيائهم مساجد».

Ahmad ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roki Ubangijinsa da kada Ya maida kabarinsa tamkar gunkin da mutane suke bauta masa ta hanyar girmama shi, da fuskantarsa a cikin sujjada, sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanar da cewa Allah Ya nisantar Ya kore wanda ya maida kaburburan Annabawa masallatai daga rahamarsa' domin maida su masallatai sila ce zuwa bauta musu da kuma kudircewa a cikinsu.

Ma"anonin Kalmomi

وثنًا: والوثن كل ما عبد من دون الله كالقبور والأشجار والحيطان والأحجار ونحوِها.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Ketare iyaka ta shari'a a cikin kaburburan Annabawa da salihan bayi ya maida su ana bauta musu koma bayan Allah, to kiyayewa daga hanyoyin shirka ya wajaba.

Nufin kaburbura dan girmama su ba ya halatta da kuma yin ibada a gurin su duk yadda kusancin masu su yake ga Allah - Madaukakin sarki -.

Haramcin gina masallatai akan kaburbura.

Haramcin sallah a wurin da kaburbura suke koda bai yi gini ba saidai sallar jana'izar da ba'a yi wa gawar sallah ba kadai.

Manazarta

Musnad Ahmad (12/ 314) (7358).

Kari (12)

فتح المجيد شرح كتاب التوحيد.

لعبد الرحمن التميمي (1/ 434).

القول المفيد على كتاب التوحيد.

لمحمد بن عثيمين (1/ 434).

الملخص في شرح كتاب التوحيد.

لصالح الفوزان (ص178).

الجديد في شرح كتاب التوحيد.

لمحمد القرعاوي (ص194).

التمهيد لشرح كتاب التوحيد.

لصالح آل الشيخ (ص51).

مشكاة المصابيح.

للتبريزي (1/ 234).