Skip to content

Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

"Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya".

«لاَ تَتَّخِذُوا الضَّيْعَةَ فَتَرْغَبُوا فِي الدُّنْيَا».

Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
Hasan ne da wani Sanadin
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga riƙon gona; domin hakan yana daga sabubban kwaɗayi a duniya da karkata zuwa gareta abar lahira.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Hani akan yawaita neman duniya da abinda yake kaiwa zuwa juyawa lahira baya.

A cikin hadisin babu hani daga riƙon binda yake akwai abin samun rayuwa daga gare shi, kaɗai hani ne daga dulmiya a cikin duniya da kuma mantawa da lahira.

Sindi ya ce: Abin nufi: Kada ku zirfafa a cikin riƙon gona sai ku shagalta da ita daga ambatan Allah.

Manazarta

Sunan Tirmizi (4/ 155) (2328).

Musnad Ahmad (6/ 54) (3579).

Kari (3)

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (331/7).

شرح رياض الصالحين لابن عثيمين (375/3).